Ƴan Bindiga Da Wanda Ke Siyar Musu Da Muggan Kwayoyi Sun Shiga Hannun Jami'an Tsaro A Ƙananan Hukumomin Illela, Rabah Da Kuma Goronyo Na Jihar Sokoto.

Ƴan Bindiga Da Wanda Ke Siyar Musu Da Muggan Kwayoyi Sun Shiga Hannun Jami'an Tsaro A Ƙananan Hukumomin Illela, Rabah Da Kuma Goronyo Na Jihar Sokoto.

Rundunar ƴan sanda a ranar Litinin ta ce ta kama ƴan bindiga 54, ciki har da mai sayar da muggan kwayoyi zuwa ga ƴan bindigar, Samuel Chinedu, a jihar Sakkwato.

 A wani taron manema labarai da mataimakin Sufeto Janar na ƴan sanda Zaki Ahmed ya yi, rundunar ƴan sandan ta ce an kashe wasu ƴan bindiga 23 a wasu ayyuka daban-daban a fadin jihar.

An kuma samu nasarar kwato bindigogi kirar AK-47 guda 32 da RPG guda biyu da kuma roka daya daga hannun ƴan bindigar.

 Mista Chinedu wanda ke siyar musu da kwayoyi, ƴan sanda sun ce an kama shi ne a otal din Pinnacle, a lokacin da yake jiran karbar kudaden muggan kwayoyi da ya kai wa ƴan bindigar.

 Ya shaida wa ƴan jarida cewa ya baiwa ƴan bindigar da ke ta’addancin jihar muggan kwayoyi masu tasiri ga aikata laifuka, ciki har da Pentazocine kan kudi N18,500 kafin a kama shi.

 Daga cikin wadanda aka kama akwai Musa Kamarawa, wanda ya saya wa shugaban ƴan bindiga Halilu Kachalla mota kirar Naira miliyan 28.5; da wani ma’aikacin lafiya, Abubakar Hashimu Kamarawa, wanda ya yi jinyar shugaban ƴan bindiga Bello Turji bayan da sojoji suka raunata shi.

DIG Zaki ya ce an kuma kwato alburusai guda 2,600 da shanu 150 da kuma wayoyin Techno 16 daga hannun ƴan bindigar.

 Shugaban ƴan sandan ya bayyana cewar ƴan fashin na daga cikin wadanda suka addabi jihohin Sokoto, Zamfara da Kebbi.

 Ya ce jami’an tsaro sun farmaki ƴan bindigar ne a sansanonin su daban-daban da suka warwatsu a kananan hukumomi uku Illela, Rabah da Goronyo a jihar.

 Ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin bayan kammala bincike.




#JaridarSokoto

Comments

Popular posts from this blog

OTTACHAIN