Posts

OTTACHAIN

Ottochain yana ɗaya daga cikin Airdrops da muke sa ran zasu fashe a wannan December din, sun ware kaso mai yawa daga coin ɗinsu domin su raba shi ga community nasu, kamar dai yadda kuka sani, taimakon juna akeyi, mu taimakawa project yana jariri har ya girma, idan ya girma sai yayi rewarding na mutane. Suma nasu haka ne. Sunzo da Quest da akeyi a Z£aly wanda suke bayar da XP, wannan points din zasu duba su ga yawan Coins din da zasu baka idan anyi mainnet. A takaice ga yadda zakayi: 1. Kayi Extension din Metamask wallet a Mises Browser, idan akwai ba sai ka sake ba. 2. Ƙa'ida sai an biya ake bada l!nk ɗin, amma zan bayar dashi a KYAUTA ga mutane. Da farko ku danna wannan l!nk.👇🏻 https://zealy.io/c/ottochain/invite/IRC6yVcRV9RqDnY3nwa2u 3. Sai kayi connecting na wallet ɗinka da site ɗin, kayi Quest ɗin da suke available, kayi claimin na points ɗinka. Shikenan sai mu jira Mainnet ɗinsu, Allah yasa muna da rabo.

Ƴan Bindiga Da Wanda Ke Siyar Musu Da Muggan Kwayoyi Sun Shiga Hannun Jami'an Tsaro A Ƙananan Hukumomin Illela, Rabah Da Kuma Goronyo Na Jihar Sokoto.

Image
Ƴan Bindiga Da Wanda Ke Siyar Musu Da Muggan Kwayoyi Sun Shiga Hannun Jami'an Tsaro A Ƙananan Hukumomin Illela, Rabah Da Kuma Goronyo Na Jihar Sokoto. Rundunar ƴan sanda a ranar Litinin ta ce ta kama ƴan bindiga 54, ciki har da mai sayar da muggan kwayoyi zuwa ga ƴan bindigar, Samuel Chinedu, a jihar Sakkwato.  A wani taron manema labarai da mataimakin Sufeto Janar na ƴan sanda Zaki Ahmed ya yi, rundunar ƴan sandan ta ce an kashe wasu ƴan bindiga 23 a wasu ayyuka daban-daban a fadin jihar. An kuma samu nasarar kwato bindigogi kirar AK-47 guda 32 da RPG guda biyu da kuma roka daya daga hannun ƴan bindigar.  Mista Chinedu wanda ke siyar musu da kwayoyi, ƴan sanda sun ce an kama shi ne a otal din Pinnacle, a lokacin da yake jiran karbar kudaden muggan kwayoyi da ya kai wa ƴan bindigar.  Ya shaida wa ƴan jarida cewa ya baiwa ƴan bindigar da ke ta’addancin jihar muggan kwayoyi masu tasiri ga aikata laifuka, ciki har da Pentazocine kan kudi N18,500 kafin a kama shi....